Najeriya ta janye daga kwallon zakaru

Shugaban hukumar kwallon Najeriya, Aminu Maigari
Image caption Najeriya ce ta dauki kofin nahiyar Afrika na shekarar 2013

Najeriya ta janye daga shiga gasar cin kofin kwallon kafa na zakarun nahiyar Afrika, saboda matsalar rashin kudi.

Shugaban hukumar kula da kwallon kafa na kasar Aminu Maigari, ya tabbatar wa BBC hakan.

A watan Yuni mai zuwa ne dai kasar zata kara da Cote d'Ivoire, a wasan cancantar shiga gasar.

'Yan wasan cikin gida na kungiyar ne ke shiga gasar, wanda za a yi a farkon shekara mai zuwa a kasar Afrika ta Kudu.

Rashin kudin ne dai ya kai ga rage ma'aikatan hukumar kwallon kafar da basu da muhimmanci.

Yayin da wasu rahotanni ke cewa an zaftare rabin albashin mai horar da 'yan wasan kungiyar Super Eagle ta kasar, wato Steven Keshi.