Ferguson ya soki wasannin sada zumunta

Manchester united
Image caption Sir Alex Ferguson

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Sir Alex Ferguson ya soki yadda ake tsara wasannin sada zumunta bayan da kocin kungiyar kwallon kafa ta Ingila Roy Hodgson ya yi zargin cewa manajojin kulob-kulob basa sakar masu yan wasa a lokacin da za'a buga wasan sada zumunta.

" A shekaru goma da suka gabata ana buga wasannin sada zumunta ne a ranar larabar kafin a shiga sabuwar kakar wasani." a cewar Ferguson.

Ya kuma ce ana buga wasannin ne a dai dai lokacinda da su kansu kungiyoyin ke bukatar 'yan wasansu.

"Banida matsala da wasannin kungiyoyin kwallon kafa amma tsari ne ba zai yu ba a karkashin wasannin sada zumunta".

Tun bayan lokacinda Hodgson ya zaman kocin kungiyar kwallon kafa ta Ingila ranar daya ga watan Mayu na shekarar 2012, yan wasan kwallon kafa na kungiyar sun buga wasannin sada zamunta biyar ciki har da nasarar da suka yi akan kasar Italiya kwanakin uku kafin a soma kakar wasannin primiya league.