Kofin FA : Man City ta fitar da Chelsea

manchester city da chelsea
Image caption Man City na harin kofin FA na biyu a shekaru uku

Manchester City za ta hadu da Wigan a wasan karshe na kofin Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA.

Manchester City ta samu nasarar hakan ne bayan ta yi galaba a kan Chelsea da ci 2-1.

Samir Nasri ne ya fara jefa kwallo a ragar Chelsea mai rike da kofin minti 37 da wasa kafin Aguero ya kara ta biyu a minti na 47 wadda itace kwallonsa ta 15 a bana.

Demba Ba ya farfado da fatan Chelsea a minti na 66 amma duk kokarin da suka yi na ramawa bai kai ga nasara ba.

A ranar 11 ga watan Mayu ne Manchester City da ake ganin za ta dauki kofin na biyu a kakar wasanni uku za ta hadu da Wigan.

A shekara ta 2011 Manchester City ce ta dauki kofin.

Yanzu Chelsea za ta maida hankali a kan gasar Europa da kuma kammala Premier a cikin jerin kungiyoyi hudu na farko domin ta sami damar buga gasar Zakarun Turai a kakar wasanni ta gaba.

Karin bayani