An kori 'yan wasa 9 daga gasar Afrika

na'urar tantance shekarun 'yan wasa
Image caption A 2003 Fifa ta fara bincike kan amfani da na'urar tantance shekarun 'yan wasa

An kori 'yan wasa tara daga gasar wasan kwallon kafa ta 'yan kasa da shekaru 17 da ake yi a Morocco saboda sun zarta ka'idar shekarun.

Naurar tantance shekarun dan wasa ce ta tabbatar 'yan wasan uku-uku daga Congo-Brazaville da Ivory Coast da Najeriya sun wuce shekarun.

Saboda haka aka hana su sake shiga gasar.

'Yan wasan da abin ya shafa su ne Cherlevy-Diabala Carim da Hardy Binguila da Bermagin Kangou na Congo.

Sauran su ne Dagou Britto da Abdul Diarrassouba da Siriki Dembele na Ivory Coast.

Sannan kuma sai Onyinye Ndidi da Ibrahim Abdullahi da Emmanuel Asadu 'yan Najeriya.

Dukkanin kasashen an rage 'yan wasansu yanzu zuwa 18.

A shekarar 2003 Hukumar kwallon kafa ta Duniya Fifa ta fara gudanar da bincike kan amfani da na'urar tantance shekarun 'yan wasa.

Amma kuma an fara amfani da ita ne a gasar Kofin Duniya na 'yan kasa da shekaru 19 da aka yi a Najeriya.

Sakamakon da aka samu a gasar Kofin Duniya na 'yan kasa da shekaru 17 a 2003 da 2005 da kuma 2007 ya nuna cewa kashi 35 cikin dari na 'yan wasan sun wuce shekarun.