Mutane 2 sun mutu a fashewar wurin tsere a Boston

fashewa a boston
Image caption Tagwayen fashewar ta sa mutane sun rude

Akalla mutane 2 ne suka mutu wasu da dama kuma suka sami raunuka, a fashewar abubuwa a daidai layin da ake kammala tseren gudun yada-kanin-wani na Boston a Amurka.

Akwai kuma wasu rahotanin da ke cewa wasu abubuwa biyu masu karfin gaske sun fashe a birnin Boston din na Amurka.

Wasu hotuna da ake nunawa kai tsaye daga wurin da lamarin ya faru, sun nuna mutane jina-jina, ma'aikatan kiwon lafiya na yi musu magani.

Motocin daukar marassa lafiya masu yawa da na 'yan sanda da kuma na jami'an kashe gobara sun isa wurin, domin bada agaji.

An kara daukar matakan tsaro a manyan gine-gine na birnin New York.