An kashe magoya baya a Brazil

filin wasa na rio brazil
Image caption Filin wasan Olympics na Rio 2016 da aka rufe

A kashe magoya bayan wata kungiyar kwallon kafa biyu a kusa da filin wasan kofin duniya na 2014 a Brazil.

Wasu magoya bayan kungiyar da ke hamayya da klub din mutanen ne suka harbe su a ka kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka tabbatar.

Lamarin ya faru ne a yankin arewa maso gabashin kasar kusa da filin wasa na Arena Castelao wadda za a yi gasar Kofin Duniya a kasar.

Rahotanni sun ce wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Cearasun gamu da ajalinsu bayan da waso magoya bayan kungiyar Fortaleza biyu da ke cikin mota suka harbe su.

Wannan dai shi ne lamari na baya-bayan nan da ke sa shakku kan ko Brazil din za ta iya karbar bakuncin gasar Kofin Duniya ta 2014 da kuma wasannin Olympics na 2016.

Bayan jinkirin sake ginin filin wasa na Maracana inda za a yi gasar Olypics ta 2016 mai taken Rio 2016, an kuma rufe filin wasa na Joao Havelange har sai abin da hali yayi.