Newcastle za ta hukunta magoya bayanta

rikicin magoya bayan newcastle
Image caption Magoya bayan Newcastle za su fuskanci hukuncin tada rikici

Newcastle ta ce rikicin da wasu magoya bayanta su ka tayar bayan Sunderland ta yi nasara a kanta 3-0 abin kunya ne da takaici.

Kungiyar kwallon kafar ta kuma yi alkawarin hana duk wanda aka samu da hannu a rikicin mu'amulla da ita har tsawon rayuwarsa.

Yayin rikicin an lahanta 'yan sanda hudu, an kama mutane 29 an kuma dauki hoton wani mutum yana naushin dokin dan sanda.

Rikicin ya barke ne bayan wasan da Necastle ta sha kashi a gida a hannun Sunderland.

Inda wasu magoya bayan kungiyar suka yi ta jifa da kwalabe suna cinna wuta.

Yayin da 'yan sandan kan doki ke ta kokarin tarwatsa mutanen.