FBI na gudanar da bincke akan harin Boston

Hukumar FBI
Image caption Tambarin hukumar FBI

Hukumar kula da manya manyan laifuka ta FBI ta ce ta na gudanar da abun da ta kira bincike akan abun da maiyiwuwa aikin ta'addanci ne dangane da tagwayen fashe-fashen da suka afku a layin kammala gudun yada kanen wani na birnin Boston.

Mutane 3 ne suka rasa rayukansu, inda akalla wasu 100 suka samu raunika, wasu daga cikinsu munana.

Idan har aka tabbatar da wannan hari a matsayin ta'addanci, to zai kasance mafi muni irinsa da aka taba kaiwa a cikin Amurka tun harin goma sha daya ga watan satumba na shekara ta 2001.

Wakilin BBC akan harkokin tsaro ya ce masu bincike suna yin nazari akan burbushin abun da ya fashe, wadanda aka ce basu da girma kuma hadin hannu ne.

'Yan sanda sun ce suna yiwa mutane da dama tambayoyi, to amma babu wani da ake zaton yana da hannu da aka tsare.

An tsaurara matakan tsaro a birane da dama na Amurka da suka hada da New York da Washington.