Fifa za ta yanke hukuncin zaben Tanzania

sepp blatter da issa hayatou
Image caption Kwamitin bincike ya mikawa Fifa da Caf rahotansa kan zaben na Tanzania

Fifa ta ce za ta yanke hukunci a mako mai zuwa a kan rikicin zaben hukumar kwallon kafa ta Tanzania.

A ranar Larabar nan hukumar kwallon kafar ta duniya ta kammala bincike a kan lamarin.

Rikicin dai ya taso ne bayan da 'yan kwamitin zaben su ka haramta wa wani tsohon sakataren zartarwa na wata kungiya, Yanga Jamal Malizi takara.

An hana shi takarar ne bisa dalilin rashin kwarewa ta shugabanci ta tsawon shekaru 5.

Hakan kuma ya baiwa mataimakin shugaban hukumar Athuman Nyamlani damar tsayawa zaben ba tare da hamayya ba.

Shi ma tsohon sakataren hukumar kwallon kafar ta Tanzania Micheal Wambura an hana shi tsayawa takara akan cewa ba shi da amana zargin da ya musanta.

A karshen shekarar da ta wuce ne aka shirya gudanar da zaben don maye gurbin shugaba mai barin gado Leodegar Tenga wanda ba zai sake neman shugabancin ba.

Fifa ta dakatar da zaben bayan da 'yan takarar da aka hana tsayawa sun yi korafi.