Hoy ya yi ritaya saboda fargaba

chris hoy
Image caption Chris Hoy ya na ganin lokacinsa ya kare

Dan tseren keken Birtaniya da ya sami lambar yabo ta zinare shida ta Olympics Sir Chris Hoy ya yi ritaya daga wasan.

Mai shekara 37 dan Scotland Chris Hoy ana tsammanin zai shiga gasar wasannin kungiyar kasashe renon Ingila wato Commonwealth a Glasgow.

Amma ya ce ba zai shiga gasar ba wadda za a yi a 2014 saboda zai matsa wa kansa gara ya bar wa matasa.

Hoy wanda ya sami lambobin zinare biyu a wasan Olympics na Landan baya ga hudu da ya samu a wasu wasannin ya kuma dauki kofunan kasa da kasa guda 11.

Da yake bayyana ritayar tasa daga wasan tseren keken a wani taron manema labarai a Murrayfield dake Edinburgh Hoy ya ce ya yi tunani matuka kafin yanke shawarar.

Karin bayani