An Kara matakan kaucewa hari a gasar Landan

gudun famfalaki na landan
Image caption Ana ganin filin gasar gudun famfalaki ta Landan ta 2013 ya fi kowanne a tarihi

Za a girke karin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a gefen hanyoyin da za a bi na gasar gudun yada kanin wani da za a yi ranar Lahadi a Landan.

Hakan na daya daga cikin matakan tsaron da masu shirya gasar su ka dauka.

Sakamakon harin tagwayen bama-baman da aka kai a lokacin gasar gudun yada kanin wani ta Boston ranar Litinin.

Harin da ya hallaka mutane uku da lahanta wasu sama da 170.