Tennis : Wawrinka ya yi waje da Murray

murray da wawrinka
Image caption Kafin karawarsu Murray ya yi kurarin lallasa Wawrinka

Zakaran tennis na Birtaniya kuma na biyu a duniya Andy Murray ya sha kaye a hannun Stanislas Wawrinka a gasar Monte Carlo.

Wawrinka dan Switzerland na 17 a gwanayen tennis na duniya ya lallasa Murray da ci 6-1 6-2.

Murray wanda ya yi nasara a kan Wawrinka sau 8 a haduwarsu 12 bai zage ya yi wasa ba kamar yadda yake yi a haduwarsu a baya.

Rashin nasarar koma baya ne ga shirin Murray na fuskantar gasar tennis ta Faransa da za a yi a watan Mayu.

Murray ya zama na biyu ne a duniya bayan da ya sami nasara a kan David Ferrer a wasan karshe na gasar Sony da a ka yi a Miami a karshen watan Mari.

Kuma ya na saran kawar da Novak Djokovic daga matsayin na daya a Monaco.

Amma a dalilin wannan rashin nasara a Monte Carlo yanzu zai koma bayan Roger Fedrer na uku a duniya.

Shi kuma Wawrinka mai shekaru 28 yanzu zai hadu da Jo-Wilfred Tsonga na Faransa a zagaye na gaba.