Mo Farah ya janye daga gasar Gudun Fanfalaki

Image caption Mo Farah ya janye daga gasar Gudun Fanfalaki

Mai rike da Kambun zakaru dan Birtaniyan nan Mo Farah, ya janye daga gasar Gudun Fanfalaki na birnin London da za ayi.

Dan wasan mai shekaru 30 ya na amfani da tseren wannan shekarar ne don shiryawa gasar shekara ta 2014.

Farah ya shaidawa BBC cewa "shekara mai zuwa zanzo na buga cikakken wasan Fanfalakin".

Farah, ya zamo mutum na bakwai da ya samu nasarar gasar mita dubu biyar da kuma mita dubu goma a gasar wasannin tsalle-tsallen da aka yi a birnin London a shekara ta 2012.

Karin bayani