Djokovic ya doke Rafael Nadal

Image caption Novak Djokovic ya samu nasara kan Rafael

A wasan karshe na zakaru a kwallon Tennis Novak Djokovic ya doke Rafael Nadal inda ya samu nasarar daukar Kambun Monte Carlo Masters.

Wannan karon dai Novak Djokovic ya kawo karshen nasarar da Rafael Nadal ya yi ta samu a gasar Monte Carlo Masters shekaru takwas da suka wuce.

Djokovic ya yi ta kokarin wasan da farko saboda ciwon agara amma daga bisani bai nuna alamun yana da ciwo ba saboda ya yi kaka gida a wasan.

Nadal kuwa mai shekaru 26, Djokovic ya yi nasara akansa ne sau biyu ne kacal a haduwa goma sha hudu wanda duka a aka yi a shekara ta 2011.

Karin bayani