Tottenham ta lallasa Manchester City 3-1

Image caption Tottenham ta lallasa Manchester City 3-1

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta yi rawar gani a wasan da ta kara da Manchester City inda ta lallasa Manchester City da ci uku da daya.

Tun farkon wasan dai Manchester City ce ta fara cin Tottenham kwallo daya a zagayen farko kafin a zagaye na biyu Tottenham ta farke ta kuma kara kwallaye biyu.

Zura kwallaye uku a mintina shida da dakikoki ashirin; wannan na nufin wasan yana kan Tottenham ne duk kuwa da matsayin da Manchester City ke dashi a gasar.

Dan wasan Tottenham din nan Clint Dempsey ne ya fara farke kwallon sai Jermain Defoe ya kara sannan kuma sai Joe Hart.

Samir Nasri na Manchester City shine ya fara zurawa Tottenham kwallon wanda daga bisani ya zame wa City din jangwam.

Karin bayani