Fondre na Reading na shawarar barin su

Image caption Dan wasan Reading Fondre na shawarar barin kulob din

Dan gaban Kungiyar kwallon kafa ta Reading Le Fondre ba shi da tabbas ko zai ci gaba da zama a kulob din kakar wasan badi ba.

Dan wasan mai yawan zura kwallaye ga Kungiyar ya ci benchi a wasan da suka buga da Norwich ranar Asabar.

Dan wasan da yake kokawa a wata hira da BBC ya ce " ni ma kamar shauran 'yan wasa nake, ina son na buga wasanni amma a halin yanzu bana samun hakan".

A cewar sa idan almurra suka ci gaba a haka bai san abinda zai faru ba.

Karin bayani