Liverpool ta ci tarar Suarez

Image caption Liverpool ta ci tarar Suarez

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta ci tarar Luis Suarez saboda cizon dan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Branislav Ivanovic; amma Kungiyar ta ce har yanzu dan gaban na da amfani a kulab din.

Suarez mai shekaru 26, ya ciji damtsen Ivanovic a wasan da suka buga aka tashi da ci biyu da biyu.

Da aka tambayi Manajan Darakta na Kungiyar Liverpool Ian Ayre ko cizon da dan wasan ya yi zai shafi zamansa a Kulab din sai yace " aa ko daya".

Suarez din dai an taba hana shi wasanni bakwai saboda cizon dan wasan Kungiyar kwallon kafa na PSV, Otman Bakkal a watan Nuwamba na 2010.

Karin bayani