Bayern Munich ta caccasa Barcelona

bayern munich da barcelona
Image caption Rashin nasarar ita ce mafi muni da Barcelona ta yi a Turai tun 1997.

Bayern Munich ta kama hanyar zuwa wasan karshe na Kofin Zakarun Turai bayan da ta casa Barcelona 4-0 a Munich.

Wasan shi ne karawar farko tsakanin kungiyoyin kafin haduwarsu ta biyu ta karshe da za su yi a gidan Barcelona kwanaki 8 masu zuwa.

Thomas Mueller ne ya jefa kwallon farko a ragar Barcelona minti 25 da shiga fili can kuma minti na 82 ya kara kwallonsa ta biyu kuma hudu ga klub din nasa.

Gomez ne ya ci kwallo ta biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 49.

Arjen Robben ne ya ci kwallo ta uku a wasan da ake ganin Bayern ta kama hanyar zuwa wasan karshe na zakarun Turai karo na 3 a shekaru 4.

Wannan ita ce rashin nasara mafi muni da Barcelona ta yi a Turai tun lokacin da Dynamo kiev ta lallasa ta da ci 4-0.

A ranar Larabar nan ce kuma Real Madrid za ta hadu da Borussia Dortmund a nasu wasan na kusa da na karshen karawar farko.