Kamaru na neman sabon kociya

jean-paul akono
Image caption Jean-paul Akono tun a watan Satumba ya ke zaman rikon kwarya

Kamaru ta fara shirin neman sabon kociyan dun-dun-dun na kungiyar kwallon kafar kasar da zai maye gurbin Jean-Paul Akono.

A watan Satumba ne aka nada Akono a matsayin kociyan rikon kwarya na kungiyar ta Indomitable Lions domin ya maye gurbin Denis Lavagne dan Faransa.

Akono wanda ya ce ba shi da sha'awar neman aikin tun a lokacin ne ya ke aiki ba tare da kwantiragi ba.

Ana ganin matsayin nasa na da nasaba ne da matakin kamfanin Puma wanda ya ke yi wa kungiyar kasar kayan wasanta.

Kamfanin ya bukaci da a sauya kociya da sauran jami'an horadda 'yan wasan.

Baya ga haka ma kamfanin ya kuma bada sunan kociyan da ya ke so a dauka.