Mario Gotze zai koma Bayern

mario gotze
Image caption A shekara ta 2009 Mario Gotze ya fara buga wasa a lig din Jamus

Mario Gotze zai zama dan wasan kwallon kafar da ya fi tsada a tarihin Jamus idan ya koma Bayern Munich daga Borussia Dortmund a kakar wasanni mai zuwa.

Kungiyar Bayern Munich ta ce dan wasan mai shekaru 20 zai dawo cikinta ranar 1 ga watan Yuli bayan ya shedawa Dortmund zai bar su.

An bada rahoton cewa Bayern Za ta sayi dan wasan a kan dala miliyan 48 dai dai da fam miliyan 31.5.

Cinikin dan wasa mafi tsada a kasar ta Jamus a baya dai shi ne na Mario Gomez da Bayern ta saye shi daga Stuttgard a kan fam miliyan 26.5 a 2009.

Kociyan Dortmund Jurgen Klopp ya bayyana cewa komawar tsohon kociyan Barcelona Pep Guardiola Bayern ita ce sanadiyyar tafiyar dan wasan.

Klopp ya ce Guardiola ne ya nuna sha'awarsa ta daukan dan wasan.

Sai dai kuma klub din na Dortmund da magoya bayansa basu ji dadin tafiyar dan wasan ba.