Alex Ferguson ya jinjinawa Van Persie

Image caption Ferguson ya jinjinawa Van Persie

Mai bada horo na Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Sir Alex ferguson ya ce Robin van Persie ya yi babbar bajintar da ba zai iya tuna wanda ya yi irin ta ba a Manchester United bayan da dan wasan ya taimaki Kulob din suka samu nasarar cin Kofin Premier.

Dan wasan mai shekaru 29, ya zura kwallaye uku a ragar Aston Villa; abinda ake kira hat-trick a turance.

Dan wasan ya zura kwallaye 24 a gasar tun lokacin da ya bar Arsenal a kakar wasannin bara a tsabar kudi £24m.

Sir Alex Ferguson ya ce ya tuna mai bada horo na Arsenal ya gaya masa cewa dan wasan ya fi yadda yake tsammaninsa.

Karin bayani