Dortmund ta casa Real Madrid

borussia dortmund da real madrid
Image caption Lewandowski ya zama na farko da ya ci kwallaye 4 a wasan kusa da karshe na Zakarun Turai

Borussia Dortmund ta baiwa Real Madrid kashi a karawarsu ta farko ta wasan kusa da na karshe na kofin Zakarun Turai da ci 4-1.

Wasan da aka yi a Jamus ya zo ne sa'oi 24 bayan Bayern Munich ita ma ta Jamus ta lallasa Barcelona ta Spaniya 4-0. Robert Lewandowski ne ya ciwa Dortmund duka kwallaye 4 yayin da Ronaldo ya ciwa Madrid kwallanta daya.

Minti 8 da fara wasa Lewandowski dan kasar Poland ya daga ragar Real Madrid kafin Ronaldo ya rama a minti na 43. Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne a minti na 50 Dortmund ta sami kwallonta ta biyu sannan kuma minti biyar tsakani Lewandowskin ya kara ta uku.

Can kuma a minti na 67 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka kayar da dan wasan Dortmund Reus Lewandowski ya kara ta hudun.

Kungiyar ta Dortmund ta sami nasara a dukkanin wasanninta na gasar Zakarun Turai shida da ta yi a gida.

Kuma Lewandowski wanda Manchester United da Bayern Munich ke harin dauka a kakar wasanni mai zuwa ya zama dan wasa na farko da ya ci kwallaye hudu a wasan kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai.

A ranar Laraba mai zuwa kungiyoyin za su yi karawa ta biyu ta karshe a gidan Real Madrid.