Mcllroy na da zabi a wasan Olympics

rory mcllroy
Image caption Rory Mcllroy na cikin takaddamar zabarkasar da zai wakilta a Olympics

Zakaran wasan Golf na biyu a duniya Rory Mcllroy yana da zabin ko dai ya yi wa Birtaniya ko Ireland wasa a gasar Olympics ta 2016 da za a yi a birnin Rio na Brazil.

An bayyana hakan ne duk da cewa hukumar wasan Golf ta R&A ta nuna dan wasan na iya wakiltar Ireland ne kawai.

Shugaban hukumar wasan golf ta Royal & Ancient Peter Dawson ya ce '' watakila akwai wata dokar wasan Olympics da ta ce Mcllroy zai iya wakiltar Ireland ne kawai a Rio saboda ya yi wa yankin wasa sau biyu a gasar kofin duniya.

Sai dai kuma Hukumar Olympics ta Duniya ta kawo wata doka da ta nuna cewa bayan shekaru uku da ya wakilci yankin na Ireland zai iya shiga tawagar 'yan wasan Birtaniya.

Zakaran wasan na golf ya samu kansa ne a cikin wannan takaddama saboda 'yan wasan da aka haifa a arewacin Ireland suna da zabin ko dai su wakilci Birtaniya ko kuma Ireland a wasannin Olympics.

A watan Satumba an ruwaito Mcllroy yana cewa shi kam ya fi jin cewa shi dan Birtaniya ne akan Ireland amma kuma ya ce hakan ba yana nufin kai tsaye zai wakilci Birtaniya ne ba.

A watan Janairu ya shedawa BBC cewa idan akwai tawagar 'yan wasan Arewacin Ireland zai shiga cikinta.