Chelsea ta sami karin Cole da Cahill

Ashley Cole
Image caption Ashley Cole ya murmure daga raunin da ya ji

'Yan wasan baya na Ingila Ashley Cole da Gary Cahil na cikin 'yan wasan da za su yi wa Chelsea wasa a karawar farko ta wasan kusa da karshe na kofin Europa da FC Basel.

Rabon da Cole ya yi wasa tun ranar 1 ga watan Afrilu da ya ji rauni a cinyarsa yayin da shi kuma Cahil aka yi masa aiki a guiwarsa ranar 30 ga watan Maris.

Haka shi ma dan wasan Brazil na gaba Oscar zai buga wa Chelsea duk da raunin da ya ke da shi a matsematsinsa.

Ita ma Kungiyar FC Basel ta Switzerland wadda za ayi wasan a gidanta dan wasanta na gaba Alex Frei ba zai buga ba.

Dan wasan ya yi ritaya daga buga wasa tun lokacin da kungiyar ta fitar da Tottenham inda ya kama aiki a matsayin daraktan wasanni na klub din Lucerne na Switzerland