Wenger : Arsenal za ta je gasar Zakarun Turai

Arsene Wenger
Image caption Arsene Wenger : na yi imani zamu je gasar Zakarun Turai''

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce ya yi imanin kungiyar za ta sami gurbin shiga gasar Kofin Zakarun Turai ta gaba.

Sa dai kociyan ya ce dole ne su kaucewa duk wani kuskure da zai sa su rasa maki tun da sauran kungiyoyi suma suna fafutukar samun gurbin.

Arsenal din yanzu tana matsayi na hudu a Premier gaban Tottenham da maki biyu amma kuma abiyar hamayyar tata ta na da sauran wasa daya da ba ta yi ba.

Arsenal ta kara shiga tsaka mai wuya a burin da take yi na kammala gasar ta Premier a cikin kungiyoyi 4 na gaba bayan da ta yi 1-1 da Manchester United ranar Lahadi.