Higuain zai bar Real Madrid

Gonzalo Higuain
Image caption Shugaban Real Madrid Perez ya nuna rashin gamsuwa da Higuain a bana

Gonzalo Higuain zai bar Real Madrid a karshen kakar wasanni ta bana kamar yadda babban jami'in kungiyar Jose Angel Sanchez ya bayyana.

Sanchez ya ce idan aka sayar da dan wasan mai shekaru 25 hakan zai bada damar sayo wasu 'yan gaba biyu da za su hadu da Karim Benzema.

An ruwaito Janar Manajan ya na cewa ''a babbar kungiya kamar Real Madrid ana bukatar samun kwararrun 'yan wasan gaba (lamba 9) guda biyu ko uku.

To amma yanzu akwai Benzema da Higuain.Higuain zai tafi Benzema zai tsaya wasu biyu kuma za su zo.''

Higuain dan Argentina ya ci wa Real Madrid kwallaye 14 a bana amma kuma an fi sanya Benzema da shi.

A 2007 Higuain ya koma Real Madrid daga River Plate kuma a da ana rade radin komawarsa Chelsea ko Juventus ko kuma Paris Saint-Germain.

Ana ganin Real Madrid za ta nemi Hernandez dan Mexico wanda a watan Afrilu ya yi korafi kan yadda ba a sa shi wasa sosai a Manchester United.

Haka kuma klub din an ce yana harin sayen Sergio Aguero na Manchester City da Gareth Bale na Tottenham.