Mai tsaron gidan AIK ya mutu

Ivan Turina
Image caption Ivan Turina ya mutu yana da 'ya'ya biyu mata kuma matarsa na da ciki

Mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta AIK ta Sweden Ivan Turina ya mutu ya na da shekara 32.

Ana ganin golan dan kasar Crotia ya rasu ne ya na bacci a daren Laraba.

Shugaban klub din Johan Segui ya ce ''mun san ya na da matsalar zuciya wadda tun ainahi yake da ita amma a yanzu lafiyarsa kalau.

Turina wanda ya taba yi wa kasarsa Crotia wasa sau daya a wasan sada zumunta da Hong Kong ya koma AIK ne daga kungiyar Dinamo Zagreb a 2010.

Sau tamanin da tara yana yi musu wasa kuma a wasa talatin da biyar ba a jefa masa kwallo raga ba ko da sau daya.