Banitez ya nuna hazaka a watan Afrilu

Rafael Benitez
Image caption Benitez ya jagoranci Chelsea zuwa wasan karshe na gasar Europa

Kocin riko na Chelsea Rafael Benitez ya lashe kyautar kocin da ya fi kowanne taka rawar gani a watan Afrilu a gasar Premier ta Ingila.

Banitez dan kasar Spain, mai shekaru 53, shi ne kocin Chelsea na farko da ya lashe kyautar ta wata-wata tun bayan Carlo Ancelotti a watan Afrilun 2011.

Rafael Benitez, wanda ya taba rike Liverpool a baya, zai bar kolub din a karshen kakar bana, inda magoya bayan Chelsea ke kiran Jose Mourinho ya dawo.

Ba a doke Chelsea a gasar Premier ba a watan Afrilu inda ta lashe wasanni uku a cikin hudu, Benitez ya kuma jagorance su zuwa mataki na uku a tebur.

Kafin karawar da za su yi da Manchester United a Old Traford ranar Lahadi, kocin United Alex Ferguson ya amince cewa "Benitez ya taka rawar gani a 'yan makonnin da suka wuce".

Karin bayani