CAF ta dakatar da Musa Bility

Musa Bility
Image caption Musa Bility ya yi takun saka da hukumar Caf kan batun zabe

Hukumar kula da kwalllon kafa ta Afrika CAF, ta dakatar da shugaban hukumar kwallon kafa na kasar Liberia Musa Bility daga harkokin kwallon kafa baki daya har na tsawon watanni shida.

Caf ta sanar da wannan matakin ne a shafinta na internet, inda ta ce Bility ya kaucewa ka'idojin amfani da takardun sirri.

An kuma ci tarar hukumar kwallon kafa ta kasar ta Liberia dalar Amurka 10,000.

Sai dai Musa Bility ya ce zai daukaka kara kan matakin na Caf.

Bility ya yi fafutukar ganin an sauya dokokin Caf wadanda suka baiwa shugabanta Issa Hayatou damar a sake zabensa ba tare da hamayya ba a watan Maris.

Sau biyu yana daukaka kara zuwa kotun duniya mai kula da harkokin wasanni ba tare da yayi nasara ba.

Karin bayani