Kiris Everton ta sauya tarihi da Liverpool

'Yan wasan Everton na korafin hana su kwallon da suka ci Liverpool
Image caption Everton na gaban Liverpool da maki biyar

Alkalin wasa ya hana kwallon da Sylvain na Everton ya jefa ragar Liverpool a Anfield gidan Liverpool din wadda da ta kasance galaba ta farko da ta samu a kan kungiyar tun 1999.

Bayan da Disdin ya ci kwallon da Leighton Baines ya bugo ta bugun gefe da kai yana tsammanin ya kawo karshen zaman jiran wannan nasara amma sai alkalin wasa ya ce Victor Anechebe ya tare mai tsaron gida saboda haka ya hana.

Tashi canjaras din ya sa Everton tana matsayi na 6 a bayan Tottenham ta 5 da maki 5.

Tottenham wadda take da ragowar wasanni 3 ita ce ke matsayin kungiyar da za ta je gasar Europa wato ta 5 a tebur a yanzu.

Ita kuma Everton tana da ragowar wasanni biyu idan ta kammala gasar a gaban Liverpool zai kasance karon farko da ta yi wannan kokari tun 1937.