Benitez ya ji dadin casa Man United

Rafeal Benitez
Image caption Benitez ya amince cewa ba a cikin ruwan sanyi suka doke Manchester United ba

Manajan Chelsea, Rafeal Benitez ya ji dadin casa Manchester United da kulob dinsa ya yi a ranar Lahadi.

Mai horar da ‘yan wasan na wucin gadi, ya yi imanin cewa Chelsea ta rage tazarar da aka bata, a kokarin cancantar shiga gasar cin kofin zakarun Turai, bayan doke Man U da ci 1-0.

Nasarar ta sa Chelsea ta koma mataki na uku a gasar Premier, kuma Blues za su iya kare gasar a sahun hudun farko, idan har sun doke kulob din Tottenham, a karawar da za su yi ranar Laraba mai zuwa.

“Karawar mu da Tottenham na da muhimmanci sosai, idan har muka iya doke su, to za mu zamo cikin kulob-kulob hudu na farko.” In ji Benitez.

Ya kuma kara da cewa “Maki uku da muka samu saboda doke Man United, wata babbar nasara ce.”

Idan har Chelsea ta doke Tottenham, za a bar yaran Andre Villa-Boas da maki shida a bayan Chelsea.