Fifa na neman sanya jami'an yaki da wariyar launin fata a fili

Kevin Prince-Boateng
Image caption Kevin-Prince Boateng na cikin 'yan kwamitin yaki da wariyar launin fatar

Kamitin yaki da wariyar launin fata na Hukumar kwallon kafa ta duniya na son a rika sanya masu sa ido a filayen wasanni.

Taron 'yan kwamitin da aka yi na farko ranar Litinin din nan ya bada shawarar sanya jami'ai a filayen wasanni domin lura da duk wani abu da za a yi da ya shafi wariyar launin fata.

Jami'an za su kasance ne baya ga wadanda za a sa su kuma da zasu rika lura da abin da ke faruwa a cikin fili da ma yadda alkalancin wasan ke gudana.

Za kuma a gabatar da shawarwarin hukuncin da za a yi wa duk kungiyar da ta aikata laifin wariyar launin fata da suka kunshi matakan hukunci biyu ko uku.

Hukunce-hukuncen sun hada da rage yawan maki da kuma fitar da kungiya daga gasa.

Dan wasan Ghana na AC Milan Kevin-Prince Boateng wanda ya jagoranci 'yan kungiyarsa suka fice daga fili a lokacin wani wasan sada zumunta.

kan nuna masa wariyar launin fata da magoya baya suka yi na cikin 'yan kwamitin.

A karshen watan nan na Mayu kungiyoyin dake cikin Fifa za su jefa kuri'a kan shawarwarin a lokacin babban taron hukumar na shekara-shekara.