Juventus ta lashe gasar Serie A

Juventus
Image caption Wannan ne karo na 29 da Juventus ta lashe Serie A

Masu rike da kanbun gasar Serie A ta Italiya Juventus sun sake lashe gasar a karo na 29 bayan da suka doke Palermo da ci 1-0 ranar Lahadi.

Kwallon da Arturo Vidal ya zira ce ta basu nasara a wasan inda suka bayar da tazarar maki 14 ga Napoli, wacce ta ke bin bayansu.

A yanzu saura wasanni hudu a kammala kakar wasa ta bana.

Wannan ne karo na farko da suka lashe gasar a jere cikin shekaru 10, idan aka cire gasar da suka lashe a shekarun 2005 da 2006 - wadanda aka kwace daga baya.

A yanzu sun yi tazara wurin lashe gasar Serie A da kofuna 11 fiye da kowanne kulob a Italiya.

Duk da nasarar da suka samu ta lashe League a karo na 29, sun fuskanci matsala a wasan na Palermo - bayan da alkalin wasa ya kori Paul Pogba bayan da ya tade Salvatore Aronica.

Karin bayani