Liverpool za ta yi wasa a Afrika ta kudu

Filin wasan Cape Town
Image caption Liverpool za ta yi wasa a Cape Town bayan shekaru 20

Liverpool ta sanar da cewa za ta je Afrika ta Kudu domin wasan sada zumunta da kungiyar Ajax ta Cape Town ranar 21 ga watan nan na Mayu.

Wasan na bayan kakar wasanni wanda shi ne na farko na Liverpool a Afrika ta Kudu tun 1994 za a yi shi ne a filin wasa na Cape Town kwanaki biyu bayan wasan karshe na gasar Premier.

Babban jami'in harkokin kasuwanci na klub din na Liverpool Billy Hogan ya ce ''wannan wani bangare ne na ayyukanmu na bayan kakar wasanni.

Kuma ya na nuna kudurinmu na kusantar magoya bayanmu ko ina a duniya komai nisansu da Anfield.''

Ya ce '' abin sha'awa ne ga klub din ya koma Afrika ta Kudu bayan shekaru ashirin.''

Manchester United da Tottenham na ziyartar Afrika ta Kudu akai akai domin wasannin sada zumunta na bayan kakar wasanni.