Benitez ya kare David Luiz

Rafeal da David Luiz
Image caption Manchester United ta dora alhakin korar Rafeal a kan Luiz

Kociyan Chelsea Rafeal Benitez ya kare David Luiz a kan korar Rafeal na Manchester United da alkalin wasa ya yi a karawarsu ranar Lahadi.

An ga Luiz yana dariya ne bayan da ya fadi lokacin da Rafeal ya taka shi aka bashi katin kora a kusan karshen wasan da Chelsea ta yi nasara 1-0 a Old Trafford.

Akan hakan kociyan United Sir Alex Ferguson ya ce Luiz ya fadi yana shure-shure ''kamar agwagwar da zata mutu.''

Benitez ya ce Luiz ba wai yana dariya ba ne domin yaudarar alkalin wasa ba.

''Yana yi wa magoya bayan Manchester United wadanda ke zaginsa ne dariya.''

Luiz mai shekara 26 ba zai fuskanci wani hukunci daga Hukumar kwallon kafa ta Ingila akan lamarin ba.