Wigan ta kara shiga tsaka mai wuya

Swansea ta ci Wigan
Image caption Swansea ta jefa Wigan tsaka mai wuya

Fatan Wigan na cigaba da zama a gasar Premier ya kara kasance wa cikin rashin tabbas bayan da Swansea ta bi ta gida da ci 3-2.

Roger Espinoza na Wigan shi ya fara jefa kwallo a ragar bakin a daidai lokacin tafiya hutun rabin lokaci.

Amma kuma Angel Rangel ya rama minti biyar da dawo wa daga hutun rabin lokacin, kafin kuma Wigan din ta kara ta biyu minti uku tsakani ta wajen McCarthy.

Bayan minti shida ne wato a minti na 59 sai Swansea ta sake ramawa ta hannun Itay Shecter.

A minti na 76 bakin suka samu kwallon da ta basu nasara wadda Dwight Tiendalli ya ci.

Rashin nasarar ta sa Wigan na bukatar maki uku ta tsira daga hadarin faduwa daga Premier yayin da ya rage saura wasanni biyu a gama gasar.

Yanzu Swansea na da maki 46 a matsayi na tara.