Tana kasa tana dabo ga Tottenham

Chelsea V Toottenham
Image caption 'Yan chelsea sun nuna alamun gajiya a wasan nasu da Tottenham

Chelsea ta tashi canjaras 2-2 da Tottenham a wasan da Tottenham din ke bukatar nasara ta zama ta hudu domin zuwa gasar Zakarun Turai.

Minti goma da fara wasa Oscar ya sa masu masaukin bakin a gaba da kwallon farko.

Emmanuel Adebayor ya ramawa Tottenham kwallon ana minti 26 da wasa lokacin da ya cilla wata kwallo daga wajen da'irar yadi 18 da ya tsinkayi mai tsaron gidan Chelsea ya fito.

Ramires ya sake daga ragar Tottenham kafin tafiya hutun rabin lokaci da minti 7 abin da ake ganin Chelsean ta kama hanyar nasara a wasan.

To sai dai kuma Tottenham din ta samu kanta ana saura minti goma wa'adin wasan ya cika da Adebayor ya baiwa Sigurdsson wata kwallo wanda shi kuma bai yi wata-wata ba ya sheka ta ragar Chelsea.

Yanzu Chelsea ta ci gaba da zama ta uku da maki 69 a wasa 36 da bambancin kwallaye 34.

Yayin da Arsenal ki bi mata baya da maki 67 da bambancin kwallaye 3.

Ita kuwa Tottenham ta biyar da ke fafutukar zama ta hudu domin samun damar zuwa gasar Zakarun Turai tana da maki 66 bambancin kwallaye 18.

Saura wasanni bibbiyu suka rage a gasar ta Premier yayin da kungiyoyin uku ke fafutukar samun gurabe biyun da suka rage na zuwa gasar Zakarun Turai.