QPR ta ci tarar Stephane Mbia

Stephane Mbia
Image caption Stephane Mbia ya kafe cewa ba shi ya rubuta sakon ba

Queens Park Rangers ta ci tarar Stephane Mbia saboda wani sako da aka gani a shafinsa na twitter dake nuna cewa yana son komawa tsohuwar kungiyarsa Marseille.

A bara ne dan wasan dan kasar kamaru mai shekaru 26 ya dawo QPR a matsayin musaya da Joey Barton wanda ya zo a matsayin aro.

Sakamakon faduwa daga Premier da QPR ta yi aka ga wani sako da aka aika daga shafin twitter na Mbia zuwa Barton da yake tambayarsa ko yana son dawowa klub din sa.

Sai dai kuma Mbia ya ce ba shi ya aika wannan sako ba wani ne ya yi wa shafin nasa kutse.

Amma duk da haka kungiyar ta ce duk rubutun da aka gani a shafin wani dan wasa shi ke da alhakin rubutun.

A don haka kungiyar ta ci tararsa tare da gargadinsa kan mu'amallarsa da klub din a nan gaba.