An nada Amodu daraktan Najeriya

Amodu Shaibu
Image caption Amodu Shaibu ne kocin da ya fi kowa nasara a Najeriya, inji NFF

An nada tsohon kocin Super Eagles Shaibu Amodu a matsayin daraktan tsare-tsare na tawagogin kwallon kafa na Najeriya.

Kashimawo Laloko da James Peters ne za su taimakawa tsohon kocin, dan shekara 55, wanda ya jagoranci 'yan wasan tawagar ta Super Eagles har sau hudu a lokuta daban-daban.

Aikin Amodu ya hada da sa ido a kan daukacin tawagogin 'yan kwallon kafa na kasar na 'yan shekaru daban-daban.

Kakakin Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Najeriya, NFF, Ademola Olajire, ya shaida wa BBC cewa, "Kwamitin zartarwa [na Hukumar] ya amince kuma ya rattaba hannu a kan takardar nadin Mista Amodu".

Ya kuma kara da cewa, "Kasar ta zabi wanda za a iya kira kocin Najeriya da ya fi kowa samun nasara, kuma an yi hakan ne da sa albarkar duk masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa".

Zabar Amodu da aka yi bai zo da mamaki ba bayan hukumar ta NFF ta jingine shawararta ta nada wani dan Belgium, Tom Saintfiet, a matsayin daraktan tsare-tsare a watan Yunin 2012.

A wancan lokacin dai ministan wasanni na Najeriya, Bolaji Abdullahi, ya kyankasa cewa ana jin akwai 'yan Najeriya da dama da ke da kwarewa da kuma ilimin wasan kwallon kafa a matakin can kasa, wadanda suka fi dacewa da mukamin na daraktan tsare-tsare.

Sai dai duk da nasarorin da ya samu, dangantaka tsakanin Amodu a gefe guda da masu sha'awar kwallon kafa da hukumomi a daya bangaren ta yi tsami.

A karkashin jagorancinsa Najeriya ta samu gurbin shiga Gasar 2010 ta Cin Kofin Duniya a Afirka ta Kudu, amma aka sallami Amodu duk da cewa tawagar ta hau matsayi na uku yayin Gasar Cin Kofin Afirka a Angola a 2010.

Wannan ne kuma karo na biyu da aka sallami Amodu ana shirye-shiryen tafiya Gasar Cin Kofin Duniya—a 2002 ma an kore shi bayan da najeriya ta kare a matsayi na uku a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka a Mali.