Moyes ya zama sabon kociyan Man United

David Moyes da Sir Alex Ferguson
Image caption Dukkanninmu mun amince da David Moyes inji Sir Alex

Manchester United ta tabbatar da David Moyes a matsayin sabon mai horar da 'yan wasanta da zai maye gurbin Sir Alex Ferguson.

A sanarwar da klub din ya fitar ya ce Moyes kociyan Everton a yanzu ya kulla yarjejeniyar aiki da klub din ta shekaru shida.

Sanarwar ta ce Moyes mai shekaru 50 zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuli.

A shekaru 11 da ya yi da kungiyar Everton Moyes ya farfado da ita daga matsayin kungiyar da ta ke cikin barazanar faduwa daga gasar Premier.

Ya bunkasa ta zuwa wadda ake gwagwarmaya da ita wajen neman gurbin gasar Zakarun Turai.

Sir Alex ne ya bada shawarar zaben Moyes wanda zai bar Everton bayan shekaru 11 domin maye gurbinsa kuma hukumomin klub din suka amince.