Guardiola zai fara aiki a Bayern Munich

Pep Guardiola
Image caption Tun bayan da Pep Guardiola ya bar Barcelona ya shiga dogon hutu

Pep Guardiola zai fara aikin horar da 'yan wasan Bayern Munich ranar 26 ga watan Yuni.

A watan Janairu ne aka sanar da shi a matsayin sabon kociyan zakarun Jamus a kwantiragin shekaru uku

Zai karbi aikin ne daga hannun Jupp Heynckes wanda ya jagoranci klub din ya dauki kofin lig da na kalubale na Jamus da kuma zuwa wasan karshe na Zakarun Turai na bana.

Guardiola yana hutu ne tun lokacin ya bar Barcelona a watan mayu na 2012 bayan ya dauki kofuna 14 a shekaru 4.