Mai yiwuwa Rooney ya zauna a Man U

Mai yiwuwa a shawo kan Wayne Rooney ya ci gaba da taka leda a Manchester United duk da cewa ya shaidawa kungiyar cewa yana so ya barta.

Makwanni biyu da suka wuce dan wasan na Ingila ya gana da Sir Alex Ferguson ya kuma shaidawa kocin cewa lokaci ya yi da ya kamata ya matsa daga inda yake.

Kungiyar ta United dai ta nace cewa ba za a sayar da Rooney ba, kuma nadin kocin Everton, David Moyes, ka iya sanya labarin ya sauya.

Da dan wasan mai shekaru 27 zai samu tabbaci daga Moyes cewa yana da muhimmanci a shirye-shiryen sabon kocin, mai yiwuwa ya tsawaita zamansa na shekaru tara a kungiyar ta Manchester United.

Dan wasan dai na daf da shiga shekaru biyun karshe na kwantiraginsa kuma a halin da ake ciki yanzu kungiyar ba ta da wani shiri na sabunta kwantiragin.

Amma a karkashin Moyes, wanda suka yi aiki tare a Everton, watakila Rooney ya samu karin kwarin gwiwa, musamman ma idan ya samu tabbacin cewa yana da wuri a kungiyar.