Ritayar Sir Alex asara ce —Redknapp

Sir Alex Ferguson da Harry Redknapp
Image caption Tafiyar Sir Alex (hagu) gagarumar asara ce, inji Harry Redknapp (dama)

Kocin Queens Park Rangers (QPR), Harry Redknapp, ya ce da tafiyar kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, harkar kwallon kafa a Ingila za ta tafka gagarumar asara.

A karshen kakar wasanni ta bana Ferguson, mai shekaru 71, zai yi murabus bayan ya kwashe shekaru 26 yana jagorancin kungiyar ta Manchester United—David Moyes ne kuma zai maye gurbinsa.

A cewar Redknapp: "Sir Alex na da matukar tasiri a kan masu horar da 'yan wasa da dama. Ya yi nasarar cimma abubuwa da yawa.

"Davey [David Moyes] kwararren koci ne. Abu ne mai kyau da wani koci dan Burtaniya zai maye gurbin [Ferguson]".

Ranar 1 ga watan Yuli Moyes zai fara aiki a Old Trafford bayan ya sanya hannu a kan kwantiragin shekaru shida ranar Alhamis--zai bar Everton ne bayan ya yi shekaru 11 yana horar da 'yan wasanta".

Da ma dai a karshen kakar wasanni ta bana kwantiragin Moyes zai kare.

Kocin West Ham, Sam Allardyce, ya ce Moyes ne ya fi kowa cancanta ya karbi aikin na horar da 'yan wasan Manchester United.