Odemwingie ya ce ya yi takaici a Albion

Peter Odemwingie
Image caption Peter Odemwingie ya ce bai ji dadin abin da Westbrom suka yi masa ba

Dan wasan gaba na West Bromwich Albion, Peter Odemwingie, ya bayyana dalilan da suka sa ya ke so ya bar kungiyar, yana mai cewa watanni hudun da suka gabata su ne mafi muni da ya gani.

A wata hira da ya yi da jaridar Birmingham Mail, dan wasan ya ce, "Ina jin wadannan ne watanni hudu mafiya muni a rayuwata".

Odemwingie ya kuma ce a shirye yake ya bayar da fam miliyan daya daga aljihunsa in har yin hakan zai sa a kyale shi ya bar West Brom ya koma Queens Park Rangers (QPR).

A da dai babu dan wasan da ke da farin jini a wajen magoya bayan kungiyar ta West Brom kamar Odemwingie, amma yanzu duk sun bi sun tsane shi.

Dan wasan na Najeriya ya ce ajiye shi a benci, da sanya shi ya buga wasa a matsayin da ba na shi ba, da ma rashin jituwa tsakaninsa da abokan wasansa a kungiyar su ne suka sa yake so ya bar West Brom.

"Ban ji dadi ba da suka ki mutunta shawarar da na yanke ta tafiya saboda na yi amanna na yi musu kokari a 'yan shekaru", inji Odemwingie.

Ya kuma kara da cewa, "Na kuma tabbatar da cewa tayin da na kawo musu ya isa ya samawa kungiyar wanda zai maye gurbi na, tunda ya rubanya abin da aka ba ni da na zo Albion.

"Amma saboda magoya bayan Albion su na ganin kamar na wayi gari ne kawai na ce ina so in bar kungiyar, kungiyar da daukacin mutanen da ke filin wasanta ke rera waka da suna na, kungiyar da ke makwabtaka da mata ta, suna ganin ina jin dadin zama...saboda haka da na ce zan tafi suke ganin na tabu".

QPR dai ta yi tayin sayen Odemwingie a kan kudi fam miliyan uku, amma Albion ta ki tana neman kari.

A cewar Odemwingie, "Na shaidawa daraktan tsare-tsare [na Bromwich Albion Dan Ashworth] cewa; 'kun samu dan wasan gaba (Romelu Lukaku) wanda ke ci muku kwallaye, ni kuma sau da yawa ina benci, kuma kungiyar na yin nasara ko ba ni.

"Saboda haka wannan dama ce a gare ni in je inda ake matukar bukata ta.

"Ranar 31 ga watan Janairu QPR ta yi tayin bayar da fam miliyan uku, amma suka ce sai dai idan za ta bayar da miliyan uku da dubu dari biyar ni kuma in kara fam dubu dari bakwai a kan haka daga cikin albashi na".