Wigan ta lashe kofin FA na Ingila

Wigan ta lashe kofin FA na Ingila
Image caption Wannan ne karo na farko da Wigan ta lashe kofi a tarihinta

Kulob din Wigan Athletic ya lashe gasar cin kofin FA na Ingila bayan da ya yi bazata inda ya doke Manchester City da ci daya mai ban haushi.

Ben Watson ne ya shigo a zagaye na biyu inda ya zira kwallon daya tilo a minti na 91.

Wannan ne kofi na farko da Wigan suka lashe a tarihinsu na shekaru 81 da kafuwa.

An baiwa dan wasan Manchester City Pablo Zabaleta jan kati ana gab da tashi daga wasan wanda aka kara a filin wasa na Wembley.

Wigan na fadi-tashin kare matsayinta a gasar Premier sai dai babu wani kulob da ya taba lashe gasar FA sannan kuma ya fadi daga gasar Premier a kakar wasanni guda.

Manchester City ce ta biyu a teburin gasar Premier kuma suna daya daga cikin kungiyoyin da suka fi kudi a duniya.

Karin bayani