Kalaman wariyar launin fata a Italiya

AC Milan
Image caption Kocin AC Milan ya yi Allah wadai da abin da ya faru

An dakatar da wasan gasar Serie A ta Italiya tsakanin AC Milan da AS Roma na wani dan lokaci saboda furta kalaman wariyar launin fata ga wasu 'yan wasan Milan.

Alkalin wasan ne ya dakatar da shi a farkon zagaye na biyu bayan da magoya bayan Roma suka rinka kalaman wariyar launin fata ga 'yan wasan Milan bakake cikin har da Mario Balotelli na Italiya.

Kyaftin din Roma Francesco Totti, ya yi korafi ga alkalin wasan, sannan ya je ya nemi magoya bayan da su daina.

Daga nan ne aka ci gaba da wasan.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Italiya ta bullo da sabbin dokoki domin shawo kan matsalar, bayan da dan wasan Milan Kevin-Prince Boateng ya fice daga filin wasa tare da abokan wasansa sakamakon kalaman wariyar da aka furta masa.

Karin bayani