Sir Alex ya kammala da nasara

Sir Alex ya yi wasan karshe da nasara
Image caption Sir Alex ya dauki kofuna 38 a Old Trafford

Kociyan Manchester United mai barin gado Sir Alex Ferguson ya kammala wasansa na karshe da nasara kamar yadda wasu da dama suka yi a baya.

Kwallon da Rio Ferdinand ya ci wadda ita ce ta farko a shekaru 5 ta baiwa Ferguson maki ukun a kan Swansea City a wasansa na 723 a Old Tarfford.

Wasan da aka tashi 2-1 Javier Hernandez ne ya fara sa Man United gaba da kwallonsa minti 39 da wasa kafin Michu ya ramawa Swansea a minti 49.

Saura minti uku wa'adin wasan na minti 90 ya cika sai Ferdinand ya ci kwallo ta biyun.

A karshen wasan ne aka yi bikin mikawa Manchester United kofin na Premier na 13 wanda ya kawo karshen shekaru 26 na Sir Alex a klub din.

Nasarorin Sir Alex

A sauran wasannin na Premier da aka yi Lahadin nan

Everton 2-0 West Ham

Fulham 1- 3 Liverpool

Norwhich 4-0 West Brom

QPR 1-2 Newcastle

Sunderland 1-1 Southampton

1: Lambar girmamawa ta sarauniyar Ingila

2: Kofunan Zakarun Turai da bayern Munich a 1999 da kuma Chelsea a 2008

5: Kungiyoyin da ya yi wa kociya- East Stirling 1974, St Mirren 1975-78, Aberdeen 1978-1986, Scotland 1985-86, Man United 1986-2013

6: kungiyoyin da ya yi a matsayin dan wasa Queens Park, St Johnstone, Dumfermline, Raangers, Falkirk, Ayr

9: Kofunan FA na Scotland da Ingila

17: Wasannin da aka haramta mishi zuwa bakin fili

26: shekarunsa a tun lokacin da United ta dauki kofn kafin nasarar Ferguson a 1993

38 : yawan kofunan da ya dauka a Old Trafford

49: yawan Kofunan da ya dauka a matsayin koci da Man U da Aberdeen da St Mirren

104: Yawan 'yan wasan da ya sayo a Man United na karshe shi ne Zaha daga Crystal palace

170: yawan kwallayen da ya ci a matsayin dan wasa

370: yawan wasan da ya buga

1499 :yawan wasanninsa da manchester United, ya yi nasara a 895, canjaras sau 337, rashin nasara sau 267

Shi ma Paul Scholes wanda ya dawo ruwa bayan ya taba yin ritaya wasan na jiya na zama na karshe a gare shi inda ya sake sanar da ritayarsa bayan da ya yi wasa 498 na Premier ya ci kwallaye 107.

A karshen wasan na jiya wanda shi ne na 717 da ya bugaw Man United shi ma an yi masa ban kwana a Old Traffod din.