Nadal ya dauki kofin Gasar Madrid Open

Rafeal Nadal ya yi nasara a Madrid
Image caption Sau tara Nadal yana galaba a kan wawrinka

Rafeal Nadal ya yi nasara a kan Stanislas Wawrinka da maki 6-2 6-4 ya dauki kofin gasar tennis ta Madrid Open.

Wannan shi ne karo na uku da dan wasan dan kasar Spaniya ya ke daukar kofin gasar kuma shi ne kofi na biyar da ya dauka a shekarar nan tun bayan da ciwon guiwar da ya ke fama da shi ya warke.

Cikin sati biyu ne kuma nan gaba dan wasan mai shekaru 26 zai fara kare kambinsa na gasar Faransa ta French open

Wanna shi ne karo na tara da Nadal ya ke samun nasara a kan Wawrinka wanda shi kuma koda sau daya bai taba yin galaba a kansa ba kuma cikin sa'a daya da mintuna 11 ya gama da shi.

Kafin wasan na jiya Lahadi Wawrinka sau tara yana nasara a jere a wasannin da ya yi.

Kuma duk da galabar da Nadal ya yi a kansa dan wasan mai shekaru 28 zai dawo cikin gwanayen tennis goma na duniya a mako mai zuwa a karon farko cikin shekaru 5.