An ci tarar kungiyar Roma dala 65, 000

An tsayar da wasan AC Milan da Roma saboda rera wakokin wariyar launin fata
Image caption Nan gaba Roma ka iya fuskantar hukuncin wasa ba tare da magoya baya a fili ba

An ci tarar Roma ta Italiya dala 65, 000 saboda cin mutunci na wariyar launin fata inda magoya bayanta suka rika rera wakokin wariya a lokacin wasanta da AC Milan na Serie A ranar Lahadi.

Kevin Prince Boateng na Ghana na daga 'yan wasan da magoya bayan suka rika yi wa wakokin.

Bayan Boateng Sulley Muntari shi ma na Ghana da Mario Balotelli na daga 'yan wasan AC Milan bakaken fata.

Sai da ta kai dai alkalin wasa ya dakatar da wasan wanda aka tashi 0-0 a kashi na biyu tsawon minti biyu aka yi wa magoya bayan magana kafin su dakatar da wakokin.

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, Fifa Sepp Blatter ya ce lamarin ya ba shi takaici ita ma kungiyar Roma ta fitar da sanarwa da take allawadai da dabi'ar magoya bayan nata.

Gargadin da aka yiwa kungiyar wanda ke hade da takardar tarar na nuni da cewa nan gaba za a iya yi wa kungiyar hukuncin yin wasa a fili ba tare da magoya baya ba idan aka maimaita abin da ya faru ranar Lahadin.