Ferguson ya nemi a marawa Moyes baya

Image caption Ferguson na son a marawa Moyes baya

Sir Alex Ferguson na son magoya bayan Manchester United su marawa David Moyes baya yayin da ya maye gurbin mai bada horo na Kulob din a wannan kakar.

Ferguson mai yin ritayar ya yi wannan rokon ne yayin da yake yin godiya ga dumbin masu son kulob din bayan wasan kusan karshe da ya yi a jiya Lahadi.

Ferguson ya zama mai bada horo na Manchester United a watan Nuwamba na 1986 amma bai dauki kambu ba sai a 1990, lokacin da suka samu nasarar kofin FA na Ingila.

Karin bayani